
Kun taɓa jin kamar kasuwa tana magana da kacici-kacici? To, labari mai daɗi: haka take, amma waɗannan kacici-kacici a zahiri tsarin jadawali ne tsarin candlestick!
Abu mafi daɗi shi ne, ba sai kun zama ƙwararru a lissafi ko gwanaye a ciniki ba kafin ku gane su. Idanunku a halitta an tsara su don gano tsari, don haka mu yi amfani da wannan ƙwarewar! Amma kafin mu shiga cikin tsarin jadawali, mu yi magana kan abubuwan da ake gina su a kai: layukan yanayin farashi na tallafi da shinge.
Layukan yanayin farashi: Ƙashin bayan tsarin jadawali
Layin yanayin farashi layi ne kawai da ke haɗa muhimman matakan farashi a jadawali, kamar farashin buɗewa na mako ɗaya ko wata ɗaya. Ku ɗauke shi a matsayin jagora da ke taimaka wa ƴan kasuwa gano yiwuwar motsin farashi. Duk lokacin da farashi ya ketare wannan layi, ana kiran hakan ɓullowar farashi (breakout), wato alamar cewa sabon yanayi na iya fara samuwa.

Tallafi da shinge su ne layukan yanayin farashi da ƴan kasuwa suka fi amfani da su.
Tallafi da shinge: Shingayen kasuwa marasa ganuwa
Matakan tallafi da shinge kamar shingaye marasa ganuwa ne waɗanda farashi ke wahalar ƙetarewa.

- Tallafi: Matakin farashi da faɗuwar farashi ke tsayawa ko farashi ya dawo sama. Ku yi tunanin ƴan kasuwa suna garzayawa su sayi kadara idan tana da arha, wanda ke hana farashi ƙara faɗuwa.
- Shinge: Matakin farashi da hawan farashi ke raguwa ko komawa baya. A nan ne ƴan kasuwa ke fara sayarwa, wanda ke hana farashi ƙara hawa.
Mu bayyana wannan da misali:
Ku yi tunanin farashin zinare ya yi ta sauka tsawon kwanaki. A dala 50 ga kowace gram, masu saye sun shigo da yawa, suna mayar da farashi sama. Wannan matakin dala 50 ya zama matakin tallafi.
Yanzu, mu ce zinare ya hau zuwa dala 100 ga kowace gram. Wasu ƴan kasuwa da suka rasa damar lokacin da farashi ya sauka sun yanke shawarar lokaci ya yi da za su sayar. Abin da ake kawowa ya fi buƙata yawa, sai farashi ya tsaya cik. Wannan matakin dala 100 yanzu ya zama matakin shinge.
Farashi kan yi ta billa tsakanin waɗannan matakai, yana samar da yanayi. Amma idan ya ƙetare tallafi ko shinge, sabon yanayi mai ƙarfi na iya bayyana — a nan ne damammaki ke buɗewa ga ƴan kasuwa!
Kayan zane: Allon zanenku na dijital don ciniki
Don gano yanayi, za ku buƙaci zana layukan tallafi da shinge a jadawalin farashinku. A nan ne kayan zane ke da amfani! Yawancin dandalin ciniki, har da Deriv Trader, suna da kayan aiki iri-iri da ke taimaka muku zana layukan yanayin farashi.

Shawarar ƙwararru: Idan kuna fara wa ne, kayan aikin Line shi ne babban abokinku. Shi ne hanya mafi sauƙi ta zana layukan yanayin farashi da fara gano tsari.
Ga misalin layukan yanayin farashi na tallafi da shinge da aka ƙirƙira ta amfani da kayan aikin Line a jadawalin candlestick na ETH/USD a Deriv Trader:

Mayar da layukan yanayin farashi zuwa dabarun ciniki dabarun ciniki
Sanin matakan tallafi da shinge kawai zai iya ba ku fifiko, amma haɗa su da tsarin jadawali na iya sa hasashenku ya fi daidaito! Gano tsari da wuri na iya taimaka muku hasashen yiwuwar motsin farashi da ɗaukar mataki daidai.
Me zai hana ku gwada ƙwarewarku? Ku buɗe asusun demo na Deriv, ku fara atisayen zana layukan yanayin farashi da gano tsari a lokacin da abubuwa ke gudana, ba tare da sa kuɗi na gaske cikin haɗari ba.
Muna muku fatan ciniki mai albarka!
Quiz
Mene ne babban aikin matakan support da resistance a jadawalin ciniki?


