Girman matsayin ciniki
Yayin da kuke shiga ciniki da Volatility Indices, fahimtar girman matsayin ciniki na zama muhimmin ɓangare na dabarar sarrafa haɗarinku. Girman matsayin ciniki yana tantance adadin jarin cinikinku da kuke ware wa kowane ciniki, yana kare ku daga asara mai yawa tare da ba ku damar amfana da damarmakin kasuwa. Ta hanyar kula da adadin jarin da kuke sakawa a hankali, za ku iya tafiyar da sauyawar farashi da ke cikin waɗannan Volatility Indices ba tare da jefa jimillar jarinku cikin haɗari ba.
Muhimmancin Girman Matsayin Ciniki
Sauyawar farashi na iya kawo damar samun riba da kuma haɗari da ke tattare da ita. Girman matsayin ciniki yana taimaka muku daidaita waɗannan abubuwa ta hanyar sarrafa yawan kasancewarku a kasuwa. Ta hanyar raba jarinku zuwa ciniki da dama, kuna rage haɗarin da ciniki guda mai asara zai yi wa asusunku gaba ɗaya babbar illa. Misali, idan kun yi asara a ciniki ɗaya, sauran jarinku da ke cikin sauran ciniki zai ci gaba da ba ku damar shiga kasuwa, wanda ke rage yiwuwar asara mai muni.
Idan kuna duba Volatility Indices daban-daban, yana da muhimmanci ku gane cewa yin ciniki da girman matsayi iri ɗaya a Volatility 10 da Volatility 250 yana sa ku fuskanci haɗari daban-daban sosai. Sauyawar farashi mafi girma na nuna ba kawai yiwuwar samun riba mai girma ba, har ma da ƙarin yiwuwar asara mai yawa. Saboda haka, daidaita girman matsayinku bisa ga sauyawar farashin Volatility Index da kuke ciniki da shi zai taimaka muku nufin samun ribar da kuke so tare da kasancewa cikin iyakar haɗarin da za ku iya ɗauka.
Dabarun Girman Matsayin Ciniki
Babu hanya ɗaya tak ta tantance girman matsayin ciniki; duk da haka, hanyoyi da dama za su iya jagorantar ku bisa ga salon cinikinku da yawan haɗarin da za ku iya ɗauka:
- Adadin dala da aka kayyade: Ku ware takamaiman adadin dala da za ku jefa cikin haɗari a kowane ciniki, kamar $10. Wannan hanya tana kiyaye haɗari iri ɗaya a ciniki da dama, wanda zai iya taimakawa wajen kare jarinku gaba ɗaya.
- Kashi na asusu: Ku zaɓi kashi na jimillar kuɗin asusunku da za ku jefa cikin haɗari a kowane ciniki. Misali, idan kuɗin asusunku $2,000 ne kuma kuna amfani da juriyar haɗari ta 1%, kowane ciniki zai jefa $20 cikin haɗari. Yayin da asusunku ke girma, wannan adadi yana daidaita kansa. Wannan hanya tana daidaita yawan kasancewarku a kasuwa da kuɗin da kuke da shi, kuma tana da amfani musamman wajen ciniki da kadarori masu sauyawar farashi kamar Volatility 250 Index.
- Girman matsayi bisa sauyawar farashi ta amfani da ATR: Alamar Average True Range (ATR) tana auna matsakaicin motsin farashin kadara cikin wani lokaci da aka zaɓa. Wasu ƴan kasuwa suna iyakance haɗarinsu zuwa ATR ɗaya a kowane ciniki. Misali, idan ATR na kwanaki 14 na Volatility 25 ya kai $8.5, za ku sa iyakar haɗarinku ya zama wannan adadi. Wannan hanya tana sa yawan kasancewarku a kasuwa ya dace da motsin farashin da aka saba gani a kowace rana, tana ba ku damar saita matakan Take Profit (TP) da Stop Loss (SL) da suka fi dacewa da yanayin kasuwa.
Ta hanyar amfani da waɗannan dabaru, za ku iya gina ingantaccen tsari na girman matsayin ciniki wanda ke dacewa da sauyawar farashin kasuwa da buƙatunku na ciniki.
Kammalawa
A ƙarshe, ƙware wajen girman matsayin ciniki yana da muhimmanci ga ciniki mai ɗorewa a Volatility Indices. Ta hanyar fahimtar haɗarin da ke cikin waɗannan kadarori da aiwatar da ingantattun dabarun girman matsayin ciniki, za ku iya kare jarinku tare da inganta damarmakin samun riba. Yayin da kuke bincika dabarun da aka tattauna a wannan darasi, ku tuna cewa babu hanya ɗaya da ta dace da kowa. Daidaita hanyar girman matsayin cinikinku da juriyar haɗarinku, salon cinikinku, da yanayin kasuwa zai ƙarfafa ku ku yi ciniki da ƙarin kwarin gwiwa.
Yanzu, kun fi shiri wajen tafiyar da duniyar Volatility Indices cikin hankali da dabara.
Quiz
Mene ne babbar manufar tantance girman matsayin ciniki?
Wace hanyar ƙayyade girman matsayin ciniki ce ke canzawa bisa sauye-sauyen kuɗin asusu?
Me manunin Average True Range (ATR) yake aunawa?


