Tsallake zuwa babban abun ciki
Darasi
5
Derivatives | Masu farawa

Taƙaitaccen bayani game da kadarorin tushe a Deriv

Tsawon lokaci
3
mintuna


A harkar ciniki da derivatives, fahimtar kadarorin tushe na cinikin derivatives yana da muhimmanci ga dabarun ciniki masu inganci. Wannan darasi zai ƙara bayyana ra'ayoyin da bidiyon ya gabatar ta hanyar ba ku cikakken bayani kan kadarorin tushe daban-daban da ake iya yin cinikin derivatives a kansu a dandalin ciniki na Deriv, ciki har da kadarorin hada-hadar kuɗi da Derived Indices na musamman. Fahimtar waɗannan kadarori zai taimaka muku yanke shawarar ciniki cikin ilimi, bisa abin da kuka fi so da kuma yadda kuke iya ɗaukar haɗari.
‍

Kadarorin Hada-hadar Kuɗi da ake iya yin Cinikin Derivatives a kansu

Deriv yana ba da kadarorin hada-hadar kuɗi masu yawa don cinikin derivatives. Wannan bambancin yana ba ƴan kasuwa damar yin amfani da damarmakin kasuwa a nau'ikan kadarori daban-daban:

  • Manyan Haɗin Kuɗin Forex: Waɗannan sun haɗa da shahararrun haɗin kuɗi irin su EUR/USD, GBP/USD da USD/JPY. Cinikin derivatives a kan manyan haɗin kuɗin Forex yakan ba da yawan ruwan kuɗi (liquidity) da ƙarancin Spreads, wanda ke sa su zama zaɓi mai jan hankali ga ƴan kasuwa da yawa.
    ‍
  • Ma'aunan Hannayen Jari: Derivatives na ma'auni suna ba ƴan kasuwa damar yin hasashe kan yadda rukunin hannayen jari ke tafiya. Cinikin ma'aunan hannayen jari na iya ba da haske kan yanayin kasuwa gaba ɗaya, tare da rage haɗarin da ke tattare da cinikin hannun jari guda ɗaya.
    ‍
  • Kuɗin Kirifto: Tare da bunƙasar kuɗaɗen dijital, Deriv yana ba da damar yin cinikin derivatives na shahararrun kuɗin kirifto irin su Bitcoin da Ethereum. Waɗannan derivatives suna ba ƴan kasuwa damar shiga wannan kasuwa mai matuƙar sauyawar farashi ba tare da buƙatar mallakar kuɗin kai tsaye ba.
    ‍
  • Kayayyakin Ciniki: Kayayyakin ciniki kamar zinare, man fetur da amfanin gona suna ba ƴan kasuwa ƙarin hanyoyin yin hasashe da kuma kare kansu daga sauye-sauyen tattalin arziƙi. Derivatives da ke bisa kayayyakin ciniki na iya yin tasiri sosai a yanayin kasuwa daban-daban.
    ‍

Fahimtar Derived Indices

Deriv yana kuma ba da Derived Indices na musamman, waɗanda ke kwaikwayon wasu halayen kasuwa tare da samar da damarmakin ciniki daban-daban:

  1. Synthetic Indices: Waɗannan ma'auni suna kwaikwayon yanayin kasuwar gaske ta hanyar amfani da amintaccen na'urar samar da lambobi na bazata. Suna ba ƴan kasuwa motsin farashi mara tsayawa, wanda ke sa su dace da dabarun ciniki daban-daban ba tare da rashin tabbacin da ake gani a kasuwannin gargajiya ba.
    ‍
  2. Basket Indices: Waɗannan ma'auni suna bin diddigin yadda tarin kadarori ke tafiya, inda suke ba da damar shiga cikin aikin rukuni gaba ɗaya maimakon dogaro da kadara guda. Misali, Gold Basket yana auna darajar zinare a kan rukunin kuɗaɗen duniya biyar. Wannan bambanta kadarori yana taimakawa wajen rarraba haɗari kuma yana iya ƙara kwanciyar hankali a ciniki.
    ‍
  3. Volatility Indices: Waɗannan ma'auni suna nuna sauyin farashi a matakan sauyawa (volatility) da aka riga aka tsara, kuma suna ba ƴan kasuwa damar amfani da motsi mai daidaito. Options a kan waɗannan ma'auni na iya jan hankali saboda tsararrun matakan haɗarinsu da iyakokin volatility da aka bayyana.
    ‍
  4. Jump Indices: Jump Indices, waɗanda nau'i ne na Volatility Indices, suna da tsalle-tsallen farashi da suka fi na yau da kullum girma, a matsakaicin sau ɗaya a kowane minti 20. Wannan siffa tana ba ƴan kasuwa damar musamman ta samun riba daga tsautsayin motsin kasuwa.
    ‍
  5. Crash da Boom Indices: Waɗannan sun dace da ƴan kasuwa da ke neman amfani da sauyin farashi na ba-zata; Crash Indices suna hawa a hankali kafin su faɗi farat ɗaya, yayin da Boom Indices ke sauka a hankali har sai sun yi tashin gwauron zabi. Waɗannan ma'auni suna ba da damarmakin ciniki bisa tsarin halayen kasuwa da ake tsammani.
    ‍
  6. Step Indices: Kamar yadda sunan ya nuna, Step Indices suna motsi cikin ƙayyadaddun matakai ko taki, wanda ke samar da yanayin ciniki mai sauƙin hasashe. Kowane mataki yana tsaye ne a ƙayyadadden adadi, wanda ke sa su jan hankali ga dabarun ciniki na ɗan lokaci da na dogon lokaci.
    ‍
  7. Daily Reset Indices: Wannan rukuni ya haɗa da ma'auni masu kwaikwayon kasuwa mai hawa ko mai saukowa cikin sa'o'i 24 (misali, Bull Market Index da Bear Market Index). Waɗannan ma'auni suna komawa ga ainihin darajarsu a farkon kowace ranar ciniki, wanda ke ba da ƙarin sauƙin hasashen yanayin yau da kullum.
    ‍

Muhimmancin Fahimtar Kadarorin Tushe

Kyakkyawar fahimtar kadarorin tushe tana da muhimmanci ga duk ɗan kasuwa da ke son samun nasara a cinikin derivatives a Deriv. Fahimtar bambancin kadarorin hada-hadar kuɗi da Derived Indices na musamman tana ba ku ilimin da ake buƙata don yanke shawara cikin hikima da kuma tsara dabarun cinikinku yadda ya kamata. Yayin da kuke ci gaba da koyo game da derivatives da amfaninsu daban-daban, ku dage wajen inganta ƙwarewarku don samun nasara a tafiyar cinikinku.

Quiz

Me ya sa Basket Indices ke da amfani wajen sarrafa haɗari?

Wane nau'in derivative ne ke bai wa ƴan kasuwa damar yin hasashe kan alkiblar gaba ɗaya ta rukunin haɗin kuɗaɗen kasuwar musayar kuɗi ko na kayayyakin ciniki?

Ta yaya Jump Indices suka bambanta da Volatility Indices na yau da kullum?

Analyse markets with AI-powered insights

Explore TradersView
WhatsApp